Kamfanin KEDCO Ya Shawarci Masu Son Karbar Guraren Haya

0
125

Sakamakon samun yawaitar bashin da ake bin masu tashi daga gidajen haya a yankunan birnin Kano, kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na Kano (KEDCO) ya shawarci masu niyyar karbar haya da su tabbatar babu bashin kudin wuta a guraren hayar da zasu karba dake jihohin Kano, Katsina da Jigawa.

Hukumar gudanarwar kamfanin tace shawarar ta zama dole ne bayan kula da ma’aikatan kamfanin dake fita aiki suka yi da kuma kaucewa gadar bashin kudin wutar da masu son karbar haya basu mora ba.

Sanarwar dake dauke da sa hannun babban jami’in kula da sadarwa na kamfanin KEDCO Ibrahim Sani Shawai tace “An lura cewa yawancin masu kama guraren haya suna yi wani kaso na kudaden wuta yayin da wasu suke biya ma kwata-kwata wanda hakan yake haifar da dumbin bashi.”

Saboda hakane muke shawartar abokan huldar mu da su dinga biyan kudin wuta cikakke domin kaucewa barin bashi mai yawa wanda zai hafar da rashin jituwa tsakanin masu son kama haya da kamfanin KEDCO.

“Sannan muna kira da masu bayar da hayar gidaje su kasance cikin tsarin biyan kudin wuta domin kaucewa samun matsala da KEDCO”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here