Shekarau Na Cikin Sanatoci 10 Dake Dumama Kujera a Majalisar Dattijai -Rahoto

0
258

Shugaban Majalisar Dattijai Ahamd Lawan, Sanata Adamu Bulkachuwa mai wakiltar Arewacin Bauchi da Taohon Gwamnan jihar Kano Sanata Ibrahim Shekarau nada dagacikin sanatoci 10 wanda basu kai kudurin doka ko guda daya ba a majalisar dattawa cikin shekara daya.

An kaddamar da majalisar dattijai ta 9 ne a ranar 11 ga watan Yuni na shekarar 2019. Tun bayan fara zaman majalisar an gabatar da kudurori 450 kamar yadda rahoton jaridar Daily Trust ya nuna.

Sauraran ragowar Sanatocin da basu gabatar da kuduri ba sun hada da : Christopher Stephen Ekpenyoung na Jami’iyyar PDP daga Akwa Ibom, Godiya Akwashiki na Jami’iyyar APC daga jihar Nasarawa, Emmanuel Yisa Orker-jev na PDP daga Jihar Benue, Kabir Abdullahi Barkiya na APC daga jihar Katsina, Nicholas Olubukola Tofowomo PDP daga jihar Edo, Peter Onyeluka Nwaoboshi na PDP daga jihar Delta da Lawali Hassan Anka na Jami’iyyar PDP daga jihar Zamfara.

Sai dai da aka tuntubi Sanata Shekarau kan rashin kai kuduri majalisar, yace yana nan yana shirin gabatar da kudurin dokar fansho a majalisar.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here