Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Mawakin da Yayi Batanci Ga ANNABI MUHAMMADU S.A.W a Kano

0
142

Daga Salisu Hamisu Ali

Kotun Shari’ar Musulunci a jihar Kano ta yanke hukuncin kisa ga wani mawaki mai shekaru 22 bayan yayi batanci ga FIYAYYEN HALITTA S.a.W.

Kotun karkashin jagorancin mai shari’a Khadi Aliyu wacce ke zaman ta a unguwar Hausawa Filin Hockey tayi hukuncin ne a yau Litinin bayan ta samu Yahaya Aminu Sharif da laifin da ake tuhumar sa.

A watan Maris ne dai Aminu Sharif ya saki wata waka wacce a ciki yayi batanci ga FIYAYYEN HALITTA S.A.w.

Wakar wacce aka sanyata a shafukan sadarwa ta jawo cece-ku-ce wanda hakan ya kai ga  tunzura matasa wajen kokarin kone gidan mawakin.

Matashin mawakin dai yana da alaqa da darikar Tijjaniyya kuma yana daga cikin yan Faira wadanda aka san su da “Fifita Sheikh Ibrahim Nyass sama da ANNABI MUHAMMAD S.A.W”.

Sai dai, yayin da suke bayyana ra’ayin su kungiyar Tijjaniya ta Jam’iyyatu Ansaridden Attijaniyya ta barranta kanta da mawakin da wakar batancin da yayi.

Babban Sakataren kungiyar na kasa Sayyidi Muhammad Aqasim Yahaya, a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, yace Darikar Tijjaniyya da Sheikh Ibrahim Nyass Masoyan ANNABI MUHAMMAD S.A.W ne.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here