Gwamnatin Kasar Nijar Ta Aika Sakon Ta’aziyya ga Jami’ar Maryam Abacha

0
185

Daga Salisu Hamisu Ali

Gwamnatin kasar Nijar tayi ta’aziyya ga mamallakin jami’ar Maryam Abacha American University dake jihar Maradi ta Kasar Nijar bisa rasuwar daya daga cikin hazikan malaman makarantar.

Sakon ta’aziyyar na dauke ne cikin wata wasika mai dauke da sa hannun ministan ilimin kasar, Malam Yahuza Salisu Madobi kuma aka aika ta ga mamallakin jami’ar Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, sannan jaridar PRIME TIME NEWS ta Same ta a yau Litinin a Kano.

Ministan wanda ya bayyana kaduwar sa da rasuwar Malam Jamilu Sambo, ya bayyana rashin mamacin a matsayin rashi ga jami’ar, kasar Nijar da ma Afrika gabadaya ba wai iya dangin sa ba.

“Gwamnagin kasar Nijar da dukkan ma’aikatan ma’aikatar ilimi na mika sakon ta’aziyyar su ga hukumar wannan makaranta tare da ma’aikatan ta bisa rasuwar daya daga cikin malaman jami’ar Malam Jamilu Sambo”, Kamar yadda wasikar ta bayyana.

Ministan yayi addu’ar Allah yasa aljanna ce makoma ga mamacin tare da bawa dangin sa hakurin jure rashin sa.

Marigayi Jamilu Sambo wanda ya rasu yana da shekaru 54 ya kasance malami a sashin koyar da ilimin halayyar dan adam na jami’ar. Sannan ya rasu ya bar mata daya da ya’ya 4.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here