Gwamnatin Kano Ta Gargadi Shugabannin Makarantun Sakandire

0
150

Daga Salisu Hamisu Ali

Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Sanusi Kiru ya gargadi shugabannin makarantun Sakandire a jihar bisa kaucewa bin ka’idojin kariya daga cutar COVID-19 a dai-dai lokacin da aka fara zana jarrabawar kammala Sakandire ta WAEC.

Idan za’a iya tunawa dai gwamnatin jihar ta sanya ranar 10 ga watan Agusta a matsayin ranar komawa makaranta ga yan ajin karshe domin basu damar zana jarrabawar kammala Sakandire.

Kwamishinan, ya fadawa Gidan Rediyon BBC Hausa da Safiyar yau cewa gwamnatin jihar tayi shiri don gudanar da jarrabawar, tare da gargadin cewa duk shugaban makarantar da ya bijirewa ka’idojin da aka shimfida za’a sallame shi.

Kwamishinan yace, gwamnati ta raba kayan kariya tare da yin feshi ga makarantu 538 da za su zana jarrabawar a jihar.

“Mun yi shiri sosai yayin da za’a fara jarrabawar WAEC. Mun samar da isassun kayan kariya.

” A wannan gaba nake jan kunne ga dukkan shugaban makarantar da ya kaucewa bin ka’idojin da aka shimfida ko ya kawo matsala ga shirin da aka yi to zamu cire shi ko ita mu tura shi ya zama mai koyarwa a aji. Inji Kwamishinan.

Sannan yace makarantu 199 ne na gwamnati zasu zana jarrabawar sai masu zaman kan sh 339.

Kwamishinan ya kara da cewa dalibai 27, 464 ne zasu zana jarrabawar .

Daga Karshe yayi kira ga dalibai suyi karatu sosai, tare da addu’a don samun nasarar jarrabawar da kuma mayar da Kano abar alfahari.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here