Gwamnatin Kano Ta Bayyana Gamsuwa da Yadda Aka Bi Tsarin Sake Bude Makarantu

0
130

Daga Muhammad Bashir

Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Malam Muhammad Sanusi Sa’id Kiru ya bayyana gamsuwa kan yadda shugabannin makarantun Sakandire suka bi ka’idojin kariya daga cutar COVID-19.

A wata sanarwa da aka aikowa jaridar PRIME TIME NEWS a yau Litinin mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar ilimi, Malam Aliyu Yusuf ta tabbatar da cigaban da aka samu.

Kwamishinan yayin da yake rangadin duba makarantun GGSS Shekara da First Lady’s collage Mariri yace abin farin ciki ne ganin yadda shugabannin makarantu suke tabbatar da anbi ka’idojin da aka shimfida a dai-dai lokacin da ake daf da fara jarrabawar kammala Sakandire.

Sannan ya bukaci dalibai da su bawa gwamnati hadin kai ta hanyar amfani da kayan kariya da aka basu tare da bada tazara, sannan ya bukaci su mayar da hankali kan jarrabawar su don samun sakamako mai kyau.

Kwamishinan ya yabawa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bisa yadda ya samar da abubuwan da ake bukata don kariya daga cutar Corona cikin gaggawa.

Sannan kuma ya yabawa yan majalisar zartarwar jihar bisa goyon bayan su don ganin an sake bude makarantun.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here