Tsaro: Buhari Ya Nemi Goyan Bayan Sarakunan Gargajiya

0
158

Daga Salisu Hamisu Ali

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana farin cikinsa tare da neman karin goyon bayan masarautun gargajiya wajen yaki da matsalar tsaro a kasarnan.

Shugaban kasar yayi nuni da irin gudunmawar da masarautun gargajiya da shugabannin addini suke bayarwa a yayin jawabi a fadar sarkin Musulmi, Sultan Abubakar na uku.

Sannan ya yaba da hadin kai da masarautun gargajiya suke bawa gwamnatin tarayya a kokarin ta na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Shugaba Buhari wanda ya samu wakilcin Ministan Shari’a na Kasa Abubakar Malami wanda ya jagoranci ministan harkokin yan’sanda Maigari Dingyadi da Babban sufeto Janar na yan’sanda na kasa Muhammad Adamu wajen daurin auren ya’yan Ambassador Shehu Malami da Marigayi Alhaji Musa Abubakar.

“Shugaban Kasa ya umarce mu da mu bayyana farincikinsa gare ka bisa goyon baya da kake bayarwa tsawon lokaci ga gwamnatin sa wajen tabbatar da tsaro da sauran matsalolin dake addabar kasar mu.” Inji Malami.

Yayin da yake jawabi, Sarkin Musulman ya bayayana goyon bayan sa dari bisa dari domin ganin nasarar gwamnatin shugaban kasa Buhari inda yace “Zamu cigaba da yin iya kokarin mu don ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here