Sarkin Kano Bayero Ya Kaiwa Sarkin Gwandu Ziyarar Girmamawa A Birnin-Kebbi

0
131

Daga Sulaiman Auwal Marshall

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya ziyarci mai martaba Sarkin Gwandu, Alhaji Dakta Ilyasu Muhammad Bashar a fadarsa dake Birnin Kebbi.

An ruwaito cewa Alhaji Aminu Bayero ya ziyarci Sarkin na Gwandu ne domin jaddada masa mubaya’a da sada zumunci.

A yayin ziyarar sarkin Kano ya bayyana irin muhimmancin da sarki da masarautar Gwandu shi ga al’ummar jihar Kano.

Cikin bayanin na mai martaba Sarkin Kano ya bayyana jin dadinsa da karbar da ya samu daga al’ummada masarautar ta Gwandu inda ya bayyana hakan da wani abu na tarihi a rayuwarsa.

Da yake karbar sarakunan Kano da Bichi, mai martaba Sarkin Gwandu, Alhaji Dr. Ilyasu Muhammad Bashar ya bayyana sarakunan da ‘yayansa masu albarka har kuma ya bukaci masu taimaka musu su jajirce domin ganin amanar dake kansu sun sauketa.

An rawaito cewa bayan kammala taron ziyarar, sarkin gwandu ya raba kyautuka ga sarakunan biyu da ‘yan majalisunsu ciki har da manyan dawakai guda biyu da sarkin ya bawa sarakunan kano da Bichi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here