Wata mata ta Canjawa Wani Yaro Addini Da Suna Zuwa Emeka A Kano- Hukumar Hisbah

0
262

Daga Sulaiman Auwal Marshall

Jami’an hukumar Hisba a jihar kano, sunyi nasarar cafke wata mata da ake zargi da yunkurin sayar da dan da ta haifa ga wadansu kabilun Igbo.

Matar mai suna Hauwa Tudun mazauniyar unguwar sabon gari, an zarge ta ne da laifin fansar da dan nata akan kudi Naira dubu dari hudu (N400,000), wanda har takai sun sauya masa suna da Addini daga Ibrahim zuwa Emeka.

Da take amsa tambayoyin manaima labarai a ofishin na Hisba, Hauwa’u ta musanta zargin da ake mata Sayar da yaron da ta haifa mai shekaru 3 da haihuwa.

Da yake jawabi Kwamandan Hisba Mai kula da karamar hukumar Fagge, Ustaz Jamilu Yusuf Fagge, ya shaidawa manema labarai yadda suka kama matar da matakan da zasu dauka akanta da zarar sun kammala bincike.

Yaci gaba da cewa a bayanan da wacce ake zargin ta basu, sun nuna cewa: wadanda ake zargi da sayan dan tuni suka gudu domin kaucewa kamun hukumar, amma duk da suna nan suna nemansu ruwa a jallo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here