Hukumar kula da sufurin jirgin ƙasa ta Samu Kudin Shiga Sama Da Biliyan 3 a shekarar 2019

0
407

Hukumar kula da sufurin jirgin ƙasa ta Najeriya wato Nigeria Railway Corporation (NRC), ta bayyana a ranar Juma’a cewa ta samu kuɗin shiga naira biliyan 3.09 a 2019 ta hanyar zirga-zirgar jiragen a faɗin ƙasar.

Mista Fidet Okhiria wanda shi ne babban daraktan hukumar, ya bayyana hakan a wata sanarwa a madadin minsitan sufuri, inda ya ce sun samu naira biliyan 1.5 ne daga jirgin Abuja zuwa Kaduna.

Okhiria ya ce jirgin Abuja zuwa Kaduna yana samar da kusan naira miliyan 130 duk wata a 2019, saɓanin miliyan 80 da aka riƙa samu a 2018.

Ya ƙara da cewa kuɗin da aka samu daga jirgin na Kaduna, an yi amfani da su ne wurin gina sauran tashoshin jirgin ƙasa a yankin Arewa kamar tashoshin Maiduguri.

“Jirgin hanyar Abuja-Kaduna ya samar da fiye da miliyan 130 duk wata, yayin da muka kashe miliyan 90 wurin biyan albashin ma’aikata da tafiyar da jirgin a tashoshin Maiduguri, waɗanda yanzu ba sa aiki saboda matsalolin tsaro,” in ji shi.

Shugaban NRC ɗin ya ce a gefe guda kuma, ɓarkewar annobar korona a Najeriya za ta shafi hasashen kuɗin da ya kamata a samu na shekarar 2020.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here