Fargaba: Masu Dauke Da Cutar COVID-19 Sama Da 1,000 Sun Gudu A Jihar Legas – Inji Kwamishinan Lafiya

0
203

 

Daga Muhammad Bashir

Gwamnatin jihar Legas tace har yanzu mutane dubu daya da dari hudu da hamsin da biyar (1,455) wadanda aka tabbatar da suna dauke da cutar COVID-19 ‘yan asalin jihar basu mika kawunansu wuraren da ake killace masu dauke da cutar na jihar ba.

Kwamishinan lafiya na jihar ta Legas, Farfesa Akin Abayomi ne ya bayyana haka ta shafinsa na twitter a ranar Lahadi, harma ya kara da cewa wadanda suka kamu da cutar har yanzu suna dauke da ita kuma za su iya yadata ga sauran al’uma.

Abayomi yace kimanin mutane 72 masu dauke da cutar Corona ne suke karbar magani a asibitocin gwamnati da na masu zaman kansu a fadin jihar.

“Ko a ranar 7 ga watan Agustan shekarar 2020 mun samu karin mutane uku da suka mutu sakamakon kamuwa da cutar ta COVID-19, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu a jihar zuwa mutane 198.”

Hukumar Dakile Yaduwar cutuka ta NCDC dai ta tabbatar da cewa ya zuwa yanzu jihar Legas nada adadin mutane 15,768 wadanda suke dauke da cutar Coronavirus, sai dai mutanen da suka samu waraka daga cutar kuma aka sallamesu yanzu sun kai 13,122.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here