Anyiwa Obasanjo Gwajin Cutar Corona

0
166

Daga Salisu Hamisu Ali

Gwajin da aka yiwa tsohon shugaban kasa Chief Olusegun Obasanjo na cutar COVID-19 sakamako ya nuna baya dauke da cutar.

Anyiwa Obasanjo gwajin ne a ranar Juma’ar da ta gabata a dakin Karatu na Obasanjo Presidential Library (OOPL) dake Pent House, Abeokuta jihar Ogun.

Mai taimakawa tsohon shugaban kasar kan sha’anin yada labarai, Kehinde Akinyemi, ne ya bayyana hakan a yau Lahadi.

Akinyemi yace gwajin wanda kwararren likita Dr. Olukunle Oluwasemowo na cibiyar gwajin cutuka ta 54gene dake Birnin Lagos yayi, sakamako ya nuna Obasanjo baya dauke da cutar.

Cibiyar dai tana daya daga cikin cibiyoyin da hukumar dakile yaduwar cutuka ta NCDC ta tantance don yin gwajin Cutar Corona.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here