Sabon Mataimakin Shugaban Jami’ar Bayero Ya Karbi Takardar Kama Aiki

0
114

Daga Salisu Hamisu Ali

Sabon mataimakin shugaban jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Abbas ya karbi takardar nadin sa a yau Asabar.

Farfesa Ibrahim Gambari, shugaban majalisar gudanarwar jami’ar ne ya mika takadar nadin sabon mataimakin shugaban jami’ar.

Gamabri shine shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa.

Farfesa Sagir Abbas ya samu nasarar zama sabon mataimakin shugaban jami’ar ne bayan ya doke yan takara uku a zaben da aka yi ranar 5 ga watan Agusta a Jami’ar ta Bayero.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here