Mai Baiwa Ganduje Shawara Kan Lamarin Addinai Ya Shiga Tsaka Mai Wuya

0
138

Mai Baiwa Gwamnan Jihar Kano shawara kan Addinai, Ali Baba Fagge ya shiga tsaka mai wuya bisa zargin datse malamai 360 kudin addu’a ta musamman da suka yi a makon da ya gabata.

Idan za’a iya tunawa dai Gwamna Ganduje a ranar Alhamis din da ta gabata ya jagoranci malamai 360 da limamai da sauran shugabanni wajen yin addu’a ta musamman wajen rokon Allah ya kare jihar da kasa baki daya daga annobar COVID-19.

Sai dai an zargi Ali Baba da yanke kudin da gwamnan yayi umarni a bawa kowanne malami na dubu 50.

Da yake musanta zargin da ake yi masa,  Ali Baba Fagge yace anyi haka ne domin baiwa wadansu sabbin malamai da aka gayyata nasu kudin addu’ar.

“Muna son kudin ne ya isa ga kowa domin haka sauran malamai za su amfana duk da gwamna Ganduje bai san da wannan cigaba ba”.

Yayin da yake bayyana ra’ayinsa kan lamarin, kwamishinan al’amarin addinai na Kano, Dr. Mohammad Tahir Baba, yace umarnin gwamnan shine ba wanda za’a zaftare ko Kobo daga dubu 50 din da aka bashi.

Itama Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da karbar korafe-korafe ta jihar Kano tace ta fara bincike akan karar da aka kaimata kan mai taiamaka gwamnan.

Shugaban hukumar Barista Muhyi Magaji ne ya tabbatar da karbar korafin daga wasu mutane.

Barista Muhyi Magaji yace korafin yayi zargin cewa mai baiwa gwamna shawara kan al’amarin addinai Ali Baba Fagge ya zaftare kudade dubu hamsin hamsin da aka bawa malamai domin suyi addu’a.

“Hukumar za tayi bincike kan lamarin kuma ba za a taba kyale wanda aka samu da laifi”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here