Ganduje Ya Taya Sabon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Edo Murna

0
122

Daga Salisu Hamisu Ali

A yayin da ake shirin kaddamar da yakin neman zaben dan takarar gwamnan jihar Edo na jami’iyyar APC, Pasto Osagie Ize-Iyamu, gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya taya murna ga sabon shugaban majalisar dokokin jihar Edo, Mista Victor Ederor.

Sannan ya aika sakon na taya murna ga sauran shugabannin majalisar da aka zaba, inda ya tabbatar da cewa sabon tsarin majalisar zai fara aiki wanda zai sanya jihar akan hanya madaidai ciya.

Ganduje ya bayyana farin cikin cewa ” zaben sabon shugaban majalisar da yan majalisar suka yi bisa tsarin doka abin cigaba ne don haka ya zama dole gare mu mu taya shi murna da sauran shugabannin majalisar.”

Sannan ya bukaci sababbin shugabannin majalisar da suyi aiki tukuru tare da yin abin da doka ta tanada”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here