COVID-19: Za’a Dawo da Zirga-Zirgar Jiragen Kasashen Ketare

0
180

Daga Salisu Hamisu Ali

Kwamitin Kar ta Kwana na Fadar Shugaban Kasa kan yaki da annobar COVID-19 ya amince da dawowa da zirga-zirgar jiragen sama tsakanin kasashen ketare da ta jirgin kasa a fadin kasarnan.

Kamfanin dillacin labarai na Kasa (NAN) ya rawaito cewa wannan yana daga cikin matakan da aka dauka bayan karewar wa’adin dokar saukaka kulle kashi na biyu.

Mista Boss Mustapha, Sakataren Gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin ne ya bayyana hakan yayin jawabin kullum-kullum da kwamitin ke gabatarwa yau a Abuja.

Inda yace ” Yana da Muhimmanci a tabbatar da cewa dakatarwar ba a janye ta gabadaya ba domin dakile yaduwar cutar.

Boss Mustapha yace yana daga cikin sauye sauyen da aka samu na takaita dokar wajen sake bude makarantu ga yan ajin karshe na makarantun Sakandire.

Shima yayin da yake jawabi Babban jami’in kwamitin, Dr. Sani Aliyu yace kwamitin ya buqaci ma’aikatar kula da sufurin jiragen sama ta fara shirye shiryen dawo da jigilar jirage zuwa kasashen ketare.

V

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here