Corona Ta Kashe Sanata Kashamu

0
164

Daga Salisu Hamisu Ali

Tsohon Dan Majalisa, Sanata Buruji Kashamu, ya rasu.

Kashamu, wanda ya wakilci mazabar Ogun ta tsakiya a majalisar dattijai daga shekarar 2015 zuwa 2019, ya rasu ne a asibitin Cardiology Consultans dake jihar Legas, kamar yadda abokin sa Murry-Bruce ya wallafa a shafin twitter.

Asibitin dai shine inda tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari suka rasu.

Rahotannin sun bayyana cewa Kashamu, wanda ke fama da ciwon Siga da hawan jini an kwantar dashi a asibitin a makon da ya gabata kafin rasuwar sa.

Kashamu, wanda ya kasance dan takarar gwamna a zaben shekarar 2019 a tutar jami’iyyar PDP, yana fuskantar tuhuma bisa zargin safarar miyagun kwayoyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here