Ana ta Kira na na Nemi Takarar Gwamnan Kano a 2023 – Kabiru Gaya.

0
138

Daga Salisu Hamisu Ali

Sanata mai wakiltar Kano ta kudu a majalisar dattawa , Sanata Kabiru Ibrahim Gaya yace yanzu lokaci ne da Kano ta kudu za ta samar da Gwamnan Kano a zaben shekarar 2023.

Kabiru wanda ya bayyana hakan yayi wani shirin gidan talabijin a Kano yace tun dawowar mulkin dimukuradiya jihar Kano ta Kudu ce kadai ba ta samu gwamna ko mataimakin gwamna daga yankin ba.

Yace yankin Kano ta tsakiya da Kano ta Arewa sun samar da gwamna shekaru 16 da shekara 8 da mataimakin gwamna shekara 4 da shekara 16.

Kabiru gaya ya kara da cewa yana kan tuntubar wadanda abin ya shafa kafin ya sanar da aniyar sa ta yin takarar gwamna.

“Ana ta kiraye-kirayen na fito takarar gwamna a shekarar 2023 ko a yau wasu matasa da dattijai daga kananan hukumomi 13 sun zo sun nemi na fito takarar gwamna bisa dalilan su na kashin kan su. Sun ce daga Kano ta Arewa suke kuma Ganduje daga yankin su yake.

” Kano ta tsakiya ta samar da Malam Ibrahim Shekaarau wanda yayi mulki tsawon shekara 8 sai Kwankwaso shima yayi shekara 8 gabaday Kano ta Tsakiya tayi shekara 16 tana mulki”. A cewar Kabiru Gaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here