WAEC Ta Fitar da Jadawalin Zana Jarrabawar ta Shekarar 2020

0
126

Daga Salisu Hamisu Ali

Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandire ta kasashen yammacin Afrika (WAEC) ta fitar da jawadalin ranakun zana jarrabawar ta shekarar 2020.

Hakanne na dauke ne cikin wata sanarwar da shugaban sashin hulda da jama’a na hukumar, Demianus Ojijeogu ya fitar.

Sanarwar ta nemi daliban da za su zana jarrabawar da suyi watsi da jawadalin lokacin zana jarrabawar dake yawo a shafukan sadarwa.

Za dai a fara jarrabawar karshe ta kammala sakandire ta kasashen yammacin Africa wato WAEC ne a ranar 17 ga watan Agusta zuwa 12 ga watan Satumba.

Sanarwar tace ” Hukumar shirya jarrabawar kammala Sakandire ta yammacin Afrika na farin cikin sanarwa da masu ruwa da tsaki, Iyayen yara da dalibai cewa an saki jadawalin zana jarrabawar na wannan shekarar.

Sanarwar ta kara da cewa “Hukumar na yin kira ga daliban da za su zana jarrabawar du su bi dokokin da aka shimfida sannan su kaucewa duk wani nau’i na satar amsa kuma su bi matakan da aka tsara na kariya daga cutar COVID-19.

Sannan hukumar tayi fatan Alkhairi ga masu zana jarrabawar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here