WAEC: Gwamnatin Kano Za ta Tsaftacce Makarantu 528

0
198

Daga Salisu Hamisu Ali

Gwamnatin jihar Kano tace za tayi feshin tsaftace makarantu 528 na gwamnati da masu zaman kan su domin tabbatar da kare lafiyar daliban da za su rubuta jarrabawar kammala Sakandire ta WAEC a jihar.

Sannan gwamnatin ta amince da sake bude makarantu ga yan ajin karshe a ranar 10 ga watan Agusta a jihar.

Kwamishinan ilimi na Jihar Kano , Muhammad Sa’id ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai yau a Kano.

Muhammad Sa’id ya bayyana cewa gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya umarci ma’aikatar muhalli da tayi feshin maganin kashe kwayoyin cutuka a makarantu domin kare lafiyar dalibai da malaman su da kuma samar da wajen yin karatu mai inganci.

Hakanan yace gwamnan ya umarci ma’aikatar lafiya da ta fara raba safar rufe hanci da baki, sabulin wanke hannu, da kayan kariya ga makarantun.

Kwamishinan ya kara da cewa gwamnatin jihar ta bada damar yin gwajin cutar COVID-19 kyauta ga dalibai da malaman makarantun gwamnati da masu zaman kan su.

Sa’id yayi bayanin cewa makarantu 528 sun hada da 199 na gwamnati da 328 masu zaman kan su wanda za’a yiwa feshin.

Kwamishinan yayi nuni da cewa mako guda da aka ware wanda zai fara daga 3 ga watan Agusta zai bawa shugabannin makarantu damar yin shirin da yakamata wajen yaki da annobar COVID-19 a makarantu.

“Ma’aikatar na kara karfin gwiwa ga makarantu wajen cigaba da koyarwa ta kafar sadarwa ta hanyar amfani da rediyo, talabijin da sauran kafafen sadarwa. Inji kwamishinan.

Yayin da yake yabawa Gwamna Ganduje Kan goyan baya da kokarin da yake ta tabbatar da shirin ilimi kyauta kuma dole kwamishinan ya kara jinjinawa masu ruwa da tsaki da kungiyoyi bisa goyan bayan da suke bayarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here