Shoprite Na Shirin Barin Najeriya

0
203

Daga Salisu Hamisu Ali

Shoprite, babban shagon siyar da kayan abinci a yankin Africa, na shirin barin Najeriya bayan wallafa yadda yake cigaba da barin hada-hadar sa a kasashen yammacin Africa.

A wani bayani da Johannesburg Stock Exchange ta sanya a kafar sadarwa a yau Litinin babban shagon siyar da kayan masarufin yace zai dakatar da cinikayyar sa a Najeriya.

“Biyo bayan kusantowar masu zuba hannun jari da yawa , da kuma sake inganta ayyukan kamfanin mu, hukumar gudanarwar kamfanin ta yanke shawarar samar da hanyoyin siyar da dukkanin siyar da shagunan ko da yawa daga cikin su” a cewar bayanan.

Shoprite dai ta fara kasuwanci a Najeriya kusan shekaru 15 da suka gabata, inda ta bude shagon ta na farko a jihar Lagos a shekarar 2005.

Wanda hakan ya kai ga tana da shaguna siyar da kayan masarufi 25 a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here