Sarki  Kauran Namoda Ya Koka Kan Matsalar Karancin Wutar Lantarki

0
120

Daga Ibrahim Sidi Kaulahi a Gusau

Sarkin Kauran Namoda dake jihar Zamfara, Sanusi Muhammad Asha yayi kukan cewa rashin wadatacciyar wutar lantarki a masarautar sa ya kasance babbar baraza ga harkokin kasuwanci a masarautar.

Sarkin ya bayyana hakanne a jiya a fadar sa dake garin Kauran Namoda yayin da yake karbar bakuncin shugabannin kungiyar samar da aikin yi da cigaban yankin Kaura Namoda wato (KANEDEF) Wadanda suka kai masa gaisuwar Sallah.

Sarkin yace garin Kaura Namoda shine gari na biyu mafi girma wajen harkokin kasuwanci a jihar ta Zamfara wacce take da tarin al’umma gami da albarkatun kasa amma bata amfanar sa sakamakon rashin wutar lantarki.

Sannan ya kara da cewa shahararren garin na Kaura Namoda wanda ya kasance tashar jirgin kasa ga yankin arwacin kasar nan yanzu na fuskantar koma baya a bangaren kasuwanci wanda tayi fice akai a shekarun baya.

“Muna harkokin aikin gona wadanda suke bukatar matsakaita da kananan yan kasuwa su bunkasa samar da abinci da kuma samar da guraben ayyuka ga matasa.

” Ina mai tabbatar wa da jama’a masarauta za ta yi kokari wajen hadin kai da duk masu ruwa da tsaki domin tabbatar da samun isasshiyar wutar lantarki wanda zai rage yawan aikata laifuka. Inji Sarkin.

Tun da farko, Sakataren Kungiyar KAEDEF Mukhtar Lawa Abubakar ya shaidawa Sarkin kokarin kungiyar na ganin an samar da wutar lantarki domin bunkasa harkokin kasuwanci tare da jawo hankalin masu zuba jari.

Shima ana sa jawabin mai magana da yawun kungiyar Abdulrazak Bello Kaura ya bayyana gamsuwa kan yadda Sarkin yake tafiyar da mulkin sa inda yace Garin na sheda kyawawan cigaba da ake samu bisa shugabancin shigar da kowa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here