Rashin Tsaro: Bazan Raba Hankali na Ba – Gwamna Sule

0
166

Daga Salisu Hamisu Ali

Gwmanan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule ya bayyana cewa bazai raba hankalin sa ba wajen shawo kan matsalolin tsaron da ake fuskanta a jihar, inda yace zai cigaba da gudanar da ayyukan cigaba a gwamnatin sa.

Injiniya Sule ya bayyana hakanne yayin da ya karbi bakuncin sarakunan jihar wadanda suka zo yi masa gaisuwar Sallah a gidan gwamnatin jihar.

Gwamnan wanda yayi amfani da damar ziyarar da sarakunan suka kai masa yayi ta’aziyyar rasuwar Mista Amos Ewa Obere sarkin yankin Odu wanda yan bindiga suka hallaka inda ya kara da cewa abin da gwamnatin sa tasa gaba shine jawo abubuwan da zu sanya jihar cigaba kuma hankalin sa bazai rabuba.

Gwamnan yayi bayanin cewa jihar ta fara samun nasara a yayin da ta zamo daya daga cikin jihohi 4 a kasar nan wajen jawo hankalin masu zuba hannun jari, sannan ta kasance daya daga cikin jihohi 22 wajen yin komai a bude da gaskiya wajen tafikar da harkokin kudi.

“Da wadannan abin farin cikin dake zuwa mana, baza mu taba barin jihar mu a dimauta ta ba, ta hanyar labaran kanzon kurege, rashin tsaro ko daga wani mutum komai girman sa.

Sannan gwamnan yayi amfani da wannan dama wajen godiya ga shugaban kasa Buhari bisa goyan bayan da yake bawa jihar a duk sanda bukatar hakan ta taso.

Injiniya Sule ya kuma jinjinawa Sarakunan bisa addu’oin su da goyan bayan da suke bayarwa ga gwamnati.

Tun da farko a jawabin sa Sarkin Lafiya kuma shugaban majalisar sarakunan jihar Justice Sidi Bage ya koka kan kisan sarkin da aka yi na baya bayan nan inda yayi kira ga gwamnan kar ya raba hankalin sa.

Sannan ya bayyana goyan bayan majalisar sarakunan ga gwamnatin jihar wajen kawo karshen matsalolin tsaro a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here