Muna Yabawa Amma Bama Cikin Farin Ciki

0
198

Daga Bala Ibrahim

Larabar satin da ya gabata 29 ga watan Yuli ne yayi dai-dai da shekaru 11 bayan kashe Muhammed Yusif, hakanan acikin watan dai na Yuli Gwamnan Jihar ta Barno Babagana Zulum ya tsallake rijiya da baya yayin da aka farmaki tawagar sa a garin Baga, a hanyar sa ta ziyartar yan gudun hijira. Sai dai masu tsaron lafiyar gwamnan sun dakile harin yayin da wasu suka ji rauni.

Hakan ya faru ne duk da yadda sojoji suka dinga bada tabbacin cewa garin Baga na cikin tsaro, a wani sakon bidiyo da ya dinga yawo a kafafen sadarwa na zamani Zulum ya soki jami’in sojan dake kula da yankin Mile 4 inda ya bayyana bacin ran sa kan yadda jami’an sojan suka kasa fatattakar yan ta’adda a yankin. “Kuna nan tsawon shekara daya , akwai sojoji 1, 181 anan da jami’ai 70, amma duk da haka mun kasa shiga garin wanda yan Boko Haram basu fi 10 ba. Idan baza ku iya rike garin Baga ba wanda yake kasa da Kilo mita 5 daga sansanin ku toh sai mu fidda rai da Baga” Gwamana Zulum yake fadawa Kwamandan Sojan.

Gwamnan da sauran jama’a da yawa a jihar suna zargin harin ba yan kungiyar Boko haram ne suka kai shi ba. Kowanne abu akan hakan zai zama abin dubawa wajen sukar sojojin wadanda suka jima suna cacar baki da gwamnan inda yake yawan sukar su wajen haifar da matsala ga al’ummar jihar ta hanyar cin hanci da rashawa. Hakika Gwanmnan ya fadawa kwamandan sojojin cewa, Muna yabawa da ku amma bama farin ciki.

Ayyukan Kungiyar Boko Haram sun fara muni ne a watan Yuli na shekarar 2009 yayin da sojojin Najeriya suka kama Muhammed Yusif wanda ya kafa kungiyar a gidan surukan sa sannan suka damka shi ga hannun jami’an yan sanda wadanda su kuma suka harbe shi a gaban jama’a a shelkwatar rundunar ya sanda ta jihar Barno. Tun daga wannan lokaci a ka kasa samun zaman lafiya a yankin arewa maso gabas da ma kasa baki daya.

Da ace Gwamna Zulum ya rasa ran sa a harin da aka kaimasa, Allah ya kiyaye in banda Allah ba wanda yasan abin da zai biyo baya. Saboda kamar yadda Mohammed Yusif yake samun biyayya ga wadanda suka yarda da shi haka Farfesa Zulum yake samun gagarumin goyan baya daga al’umma bisa jajircewar sa tare da dakile duk wani abu da zai kawo matsala ga al’ummar sa.

Tun bayan shigar sa ofis a matsayin gwamnan jihar Barno, Farfesa Zulum wanda ya hau karagar mulki bisa yarjewar Ubangiji ya sadaukar ga kan sa ga al’umma .

Yayin da Wasu musamman yan hamayya suke kallon sa a matsayin dan siyasar da jama’a suke so, wanda ya zabi yayi rayuwa kamar kowa Zulum yayi suna wajen tausayi tare da aiki ba tare da sanya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here