Hukumar EFCC ta gayyaci Murtala Sule Garo

0
337

Daga Salisu Hamisu Ali

Kwamishinan kananan hukumomi na Jihar Kano , Murtala Sule Garo yana amsa tambayoyi daga hukumar dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati bisa zargin mallakar kadarori a Kano da Abuja.

Murtala Garo yana daya daga cikin manyan jami’an gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.

Mai magana da yawun hukumar EFCC, Dele Oyewale ya tabbatarwa da jaridar Daily Nigerian labarin in da yace “Hukumar ta gayyaci Murtala Sule Garo ne ba kama shi tayi ba domin yin bayani kan wasu abubuwa guda biyu”.

Sai dai Mr Oyewale bai bayar da cikakken bayani akan binciken ba.

Wata majiya ta shaidawa jaridar DAILY NIGERIAN cewa an gayyace shi ne domin yin bayanin yadda ya samu kudade na mallakar rukunin gidaje, manyan motoci da gidajen mai da sauran su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here