
Daga Hannatu Sulaiman Abba
Gwamnatin jihar Kano ta Amince da Ranar 10 ga watan Agusta a matsayin ranar da daliban ajin karshe na makarantun sakandire zasu koma makaranta.
Kwamishinan ilimi na jihar Kano Muhammad Sanusi Kiru ne ya sanar da hakan a taron manema labarai yau a Kano.
Sannan kwamishinan ya umarci shugabannin makarantun Sakandire da su shirya karbar daliban ajin karshe na makarantun kwana a ranar 9 ga watan Agusta yayin da Daliban makarantun je ka ka dawo zasu koma 10 ga wata.
Tun a watan Maris ne dai Gwamnatin Kano ta rufe makarantu domin hana yaduwar cutar COVID-19 Sai dai a makon da ya gabata gwamnatin tarayya ta amince da sake bude makarantun Sakindire ga yan ajin karshe.