Ganduje Ya nada Farfesa Yahuza Bello Shugaban Majalisar Gudanawar Jami’ar Yusif Maitama Sule

0
172

Daga Salisu Hamisu Ali

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya amince da nadin Farfesa Muhammad Yahuza Bello mataimakin shugaban jami’ar Bayero ta Kano mai barin gado a matsayin sabon shugaban gudanarwar jami’ar Yusif Maitama Sule .

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na Kano Malam Muhammad Garba ya fitar tace Nadin Farfesa Muhammad Yahuza Bello farfesa a fannin lissafi ya fara aiki ne nan take.

Ya lashe gasar tallafin karatu ta tarayya a matsayin wanda yayi kokari na musamman a lokacin karatun digiri na uku sannan ya lashe kyautar Alhaji Aminu Dantata.

Sunan sa ne yana daga cikin dalibai mafiya hazaka wadanda suka samu A a kowanne Course yayin digirin digir-gir a shekarar 1988 a Jami’ar Arkansas.

Farfesa Yahuza Bello Ya rike mukamai daban-daban a jami’ar wadanda suka hada da shugaban sashin koyan lissafi na jami’ar daga shekarar 1991 zuwa 1999 da mataimakin shugaban jami’ar.

Hakanan Ganduje ya amince da sanyawa titin CBN Qtrs da zuwa Zaria road sunan tsohon shugaban majalisar gudanawar jami’iar ta Yusif Maitama Sule Malam Sule Yahaya Hamma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here