Boko Haram: Muna cikin Fargaba a Jihar Barno – Shehun Barno

0
243

Daga Salisu Hamisu Ali

Shehun Barno, Alhaji Garbai Elkanemi yace yanzu mazauna Barno na rayuwa cikin fargaba bisa tsoron harin yan kungiyar Boko Haram.

Alhaji Garbai Elkanemi ya bayyana yanayin da ake ciki a Maduguri yayin da yakai gaisuwar Sallah ga Gwamnan jihar Farfesa Babagana Zulum a gidan gwamnatin jihar yau Asabar.

Shehun Barnon na fadin hakanne bayan harin da aka kaiwa tawagar Gwamnan jihar a garin Baga a ranar Laraba da ta gabata da harin Bam da aka kai wanda yayi sanadiyar rasa rayukan mutane 6 da jikkata mutane 27 “akwai bukatar daukar matakai domin kare lafiya da dukiyar jama’a tare da dawo da zaman lafiya ga jihar dake fama da rikici”.

” Mai girma Gwamna bamu ji dadin abin da ya faru a garin Baga ba da sauran gurare abin takaici ne da jimami kwarai. Matukar za’a kai hari ga babban mai tsaron jiha toh wallahi ba wanda ya tsira sabida shine mai matsayi na farko” cewar Shehun Barno.

“Matukar za’a dinga kai hari ga manyan mutane a wannan jihar na maimaita babu wani mutum da zai tsira. Lamarin yayi muni, ina kira ga kowa da kowa yayi addu’a Allah ya kawo mana dauki”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here