Rundunar Yan Sanda ta Jihar Kano ta soke duk wani nau’i na Bikin Sallah

0
165

Daga Salisu Hamisu Ali

Rundunar Yan Sanda ta jihar Kano ta soke dukkanin wasu shagul-gulan Sallah wadanda suka hada da sukuwar doki, wasanni, walima da sauran su.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin rundunar yan sandan ta jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa wacce aka aikawa menema labarai a Kano ta bayyana cewa za’a cigaba da sintiri na Operation Puff-Adder domin maganin duk wata barazana daga masu aikata laifuka a jihar

Rundunar Yan sandan tace dukkan wasu rukunin mutane ko dai-daikun mutane da suka aikata wani aiki na karya doka matukar aka kama su zasu fuskancin fushin hukuma.

Hakanan rundunar tayi kira ga mutanen Kano su zama masu bin doka a yayin da aka zuba jami’an tsaro a Masallatan Idi domin tabbatar da zaman lafiya.

Yan Sanda sun kuma bayyana cewa masu zuwa masallaci ana shawartar su da su guji daukar kayayyakin da ba su zama dole ba.

“Kananan yara da wadanda basu da damar tuki ba a yarda su tuka motoci ba yayin tafiya masallacin Idi , iyayen yara su kula da ya’yan su wajen tafiya masallaci saboda samun rahotan batan yara.

Daga karshe Rundunar ta shawarci masu zuwa masallaci da su bi shawarwarin masana lafiya na bada tazara, sanya safar rufe hanci da fuska da sauran matakan kariya daga cutar COVID-19.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here