Za’a Kara Shiga Kotu Tsakanin Abba Gida Gida Da Ganduje.

0
219

Daga Salisu Hamisu Ali

Dan takarar gwamna na jami’iyyar PDP a zaben shekarar 2019 Abba Kabir Yusif ya kai karar gwammatin jihar Kano da Kamfanin Mudassir& Brothers da karin mutane uku gaban babbar kotun jihar Kano bisa zargin rarraba guraren amfanin al’umma ga dai-dai kun mutane.

Inda yace makarantar da aka yi don al’umma wacce take a tsohon Hotal din Daula an bayar da ita ga wasu tsirarun mutane.

Wadanda ake karar dai sun hada da Alhaji Mudassir Idris Abubakar, Kwamishinan shari’a na Kano .

A karar da Lauyan Abba Kabir Yusif, Bashir Yusif Muhammmad ya shigar a madadin sa ya nemi kotun ta hana duk wadanda ake karar wajen yin amfani da ginin na Daula Hotel.

Gwamnatin jihar Kano dai ta sanar da cewa ta bayar da wani bangare na Daula Hotel domin gina babban shago na zamani a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here