COVID-19: Bazan Karbi Masu Ziyarar Bikin Sallah Ba – Buhari

0
215

Daga Salisu Hamisu Ali

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace zai gudanar da Sallar idin Babbar Sallah shi da iyalin sa a gida bisa matakan da aka sanya na kariya daga cutar Corona.

A wata sanarwa da Mai taimaka masa kan kafafen yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar yace Buhari bazai karbi bakuncin ziyarar gaisuwar sallah ba.

Inda yace matakin na kan tsarin da ka’idojin da kwamitin kar ta kwana kan yaki da cutar COVID-19 ya shimfida.

“Shugaba Buhari Zai gudanar da Sallar Idin Babbar Sallah ne a gida tare da iyalan sa kamar yadda yayi a karamar Sallah bisa shawarar majalisar koli ta addinin musulunci da kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar Corona”.

” Yayin taya musulmai murnar bukukuwan Sallar shugaban Kasa yayi kira da acigaba da bin tsarin da aka shimfida na yaki da cutar” a cewar Sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa “domin hana yaduwar cutar , shugaban kasa bazai karbi gaishe-gaishen Sallah ba daga shugabannin Addini, Al’umma, da shugabannin gwamnati inda ya shawarci jama’a da su bi ka’idojin da mahukunta suka shimfida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here