Bikin Sallah: Gwamnatin Tarayya ta bada Hutu

0
187

Daga Salisu Hamisu Ali

Gwamnatin tarayya ta sanar da Ranakun Alhamis 30 ga wata da Juma’a 31 ga wata a matsayin ranar hutu domin bukukuwan Babbar Sallah.

Gwamnatin ta bayyana hakanne cikin wata sanarwa da babban sakatare a ma’aikatar harkokin cikin gida Georgina Ehuriah ya fitar.

Sanarwar tace , ministan cikin gida Rauf Aregbesola ya taya murna ga al’ummar musulmai da yan Najeriya gabadaya.

Sannan yayi kira ga musulmai da su cigaba da yada kyawawan halaye na soyayya, zaman lafiya, tausayi irin na FIYAYYEN HALITTA S.A.W Sannan suyi amfani da lokacin wajen yin addu’ar zaman lafiya da hadin kai a lokacin da duniya take fuskantar kalubalen cutar COVID-19.

Daga Karshe Ministan ya shawarci yan Najeriya su dauki matakan da aka shimfida wajen kariya daha cutar COVID-19 ta hanyar ba da tazara da sauran abubuwan da mahukunta suka sanya.
[28/07, 6:44 pm] Salisu Hamisu Poly: Za’a Kara Shiga Kotu Tsakanin Abba Gida Gida Da Ganduje………

Dan takarar gwamna na jami’iyyar PDP a zaben shekarar 2019 Abba Kabir Yusif ya kai karar gwammatin jihar Kano da Kamfanin Mudassir& Brothers da karin mutane uku gaban babbar kotun jihar Kano bisa zargin rarraba guraren amfanin al’umma ga dai-dai kun mutane.

Inda yace makarantar da aka yi don al’umma wacce take a tsohon Hotal din Daula an bayar da ita ga wasu tsirarun mutane.

Wadanda ake karar dai sun hada da Alhaji Mudassir Idris Abubakar, Kwamishinan shari’a na Kano .

A karar da Lauyan Abba Kabir Yusif, Bashir Yusif Muhammmad ya shigar a madadin sa ya nemi kotun ta hana duk wadanda ake karar wajen yin amfani da ginin na Daula Hotel.

Gwamnatin jihar Kano dai ta sanar da cewa ta bayar da wani bangare na Daula Hotel domin gina babban shago na zamani a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here