ABUN MAMAKI : Mace bata taba gama sakandari ba a garin karofin yashin Danshayi jihar Kano

0
701

Daga Hannatu Suleiman Abba

Kauye karofin Yan yashi dake Dan shayi a karamar hukumar Rimin Gado na fuskantar kalubale na rashin ingantace hanya, makaratun,Asibiti da Kuma zaizaiyar kasa ,Wanda haka yake Zama barazana ga rayuwar su.

Kauye karofin Yan yashi a Dan shayi na da iyaka da karamar hukumar madobi Wanda bai da tazara Mai nisa da babban titi madobi. Kauye na da mutane cikin sa sun haurawa dubu 5,Kuma da mazabar yin zabe ,sai dai Kuma har yau romo damokaradiyar bai Isa garesu ba,ta fanni inganta musu rayuwa,duk da kudaden da Gwannatin taraiyya da na jahar ke fitarwa domin a inganta fannoni da dama a cikin karkara a fadin kasar na.

Ruwa ne ya raba garin gida biyu

Malam Garba Acashe Wanda Daya daga cikin masu gwagwarmaya don kawo wa kauye Dan shayi dauki ya bayyana mana cewa “Har kawo yau bamu taba samu mace data gama makaratar sakandari ba duk da cewa bamu da nisa da titi madobi da zai Kai daliban cikin gari wajen neman ilimi sanadiyar barazanar da kogi kauyemu ke yi Mana,Wanda kwale-kwale ne ke daukar mu shima sai ka biya naira 20, idan Kuma baka dashi sai dai ka shiga ciki kogi kayi nutso, a sanadiyar haka mun samu asara rayuka daga Yara har manya ba iyaka a cikin kauye karofin Yan yashi na Dan shayi.

Kwale kwale da daukar mutane a garin

Hakazalika,kauye mu na sahun gaba wajen samu matsalar asibiti domin idan mace zata haihu sai dai mu sa ta a cikin kwale-kwale tare da babur din mu, domin samu Isa ga asibiti cikin birni cikin kannani lokaci gudun Kar a rasa ran mahaifiyar da jaririnta,duk da asibiti da aka yin Mana na Sha ka tafi, Wanda baya aiki a kashe mako Kuma babu isasun kayyakin.

A gefe guda Kuma,rashin wutan lantarki na cikin jerin kalubale a kauye ,domin kauye ya haura shekara 100 da kafuwa Amma bamu taba samu wutan lantarki ba,sai dai shekara 2011 ne aka saka Mana falwaya Wanda har yau ba a sake waiwayar zance wutar lantarki ba a cikin kauye.

Lokacin da ake tsallakar damu a kwale kwale

Malam Garba ya Kara dacewa matsalar zaizaiyar kasa Kuma dama kullum Akan sa muke,Wanda a haka muka ci alwashi ba Mai zuwa ya dibar mana yashi a kogi ko kasa a kauye mun na jiran Gwannatin, hukomomin da ta kawo mana dauki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here