Zamfara: Dakarun Operation Hadarin Daji sun hallaka tarin ‘yan bindiga

0
282

Daga Abubakar zaharadden

Rahotonni daga jihar Zamfara na nuni da cewa, wasu jiragen yaƙi na dakarun Operation Hadarin Daji na rundunar sojin Najeriya sun samu kashe nasarar hallaka ‘yan bindiga masu yawa a wani hari da suka kai musu.

Bayanai sun tabbatar da cewa jiragen yaƙin sun kuma lalata maboyar ‘yan bindigar a dajin Doumborou a jihar.

‘Yan bindigar da jiragen yakin suka hallaka an tsegunta cewa, suna karkashin kulawar wani gawurtaccen dan ta’adda ne da ake yi wa laƙabi da Dangote.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun shalkwatar tsaro ta kasa manjo janar John Enenche, ta ce a baya-bayan nan ne dakarun suka samu bayanan sirri game da maɓoyar ‘yan bindigar a cikin dajin lamarin da ba tare da bata lokaci ba suka kai musu hari ta sama.

Sanarwar ta kuma ruwaito cewa, manjo janar John Enenche ya ce, dakarun na operation Hadarin Daji za su ci gaba da shiga lunguna da sakuna na dazukan da ke yankin don kakkabe ‘yan ta’adda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here