Tsarin da ake bi wajen yaƙi da shaye – shaye akwai lauje cikin naɗi – Auwal Danlarabawa

0
489

Daga Abubakar zaharadden

Shugaban gidauniyar jin ƙai tare da bayar da tallafi tun daga tushe wato Grassroot Care and Aid Foundation (GCAF),Jakada Auwal Muhammad Danlarabawa ya bayyana cewa yaƙin da hukumomi su ke yi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar Kano akwai lauje a cikin naɗi, muddin idan har ba a bi wasu matakai ba.

Auwal Muhammad Danlarabawa ya bayyana haka ne a lokacin buɗe sabon ofishin bijilanti da ke unguwar Gama a yankin ƙaramar hukumar Nasarawa da ke jihar Kano.

“Da farko muna bayyana cewa matukar da gaske ake ana son hana shaye-shaye to sai an yi da gaske kuma kowa ya bayar da gudunmawa ta gaske ƙarkashin haɗin gwiwar aiki tare, da daƙile duk wata ƙofar da ake amfani da ita a samar da damar yin shaye -shaye”

“Abin da zai kawo karshen wannan shi ne a haramtawa sha a kowacce unguwa, ya zama babu wani waje da za’a sha ko da sigari ne a fili duk inda aka ga wani ko wata za zai sha a hana tun daga lunguna, ramuka,kangwaye, shaguna makarantu, gidajen kallo, gidajen Dambe, filayen wasanni, ma’aikatu, da kuma tashoshin mota”

Auwal Danlarabawa ya ce babu shakka wannan aiki za a yi shi da gamayyar hadakar yaki da shaye shaye wanda ya hada da Iyaye, ƙungiyoyi, ƴan sanda, ƴan hisba, ƴan bijilanti, Jami’an NDLEA, masu unguwanni da dagatai, da kuma Malamai.

A ƙarshe ya ce babban aikin gwamnati a wannan ɓangarr shi ne ta dakile duk wanda da ake shigo da kayan maye tarr da hana masu sayarwa, gwamnati kuma ta yi duk mai yiwuwa ta hana ƴan siyasa amfani da miyagun ƙwayoyi tare da kayan maye a wajen harkokin siyasa da ofishin jam’iyyu .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here