Talakawan ƙasar nan ba za su taɓa manta ƙangin wahalar da PDP ta jefa su ba – Mai Mala Buni

0
322

Daga Abubakar zaharadden

Ganin wasu rahotannin na nuna cewa jam’iyyar APC ta kasa na kokarin fitar da shugaban jam’iyyar ta kasa daga Arewa maso gabashin Najeriya, inda Shugaban kasa kuwa zai fito daga kudancin Najeriya, kana arewa maso yamma ta fitar da Mataimakin Shugaban kasa, Shugaban jam’iyyar APC na wucin gadi Alhaji Mai Mala Buni, kana gwamnan jihar Yobe, ya musanta hakan.

Gwamna Mai Mala Buni ya ce har ya zuwa wannan lokacin jam’iyyar bata fara wani shiri na fitar da dan takara ba.

“Nan ba da jimawa ba za’a fara wannan shirin, amma a yanzu riga Malam Masallaci ne kawai jama’a ke yi, na fitar da shugaba, babu kanshin gaskiya akan zargin da ake yi na cewar, ina goyon bayan tsayar da jigo a jam’iyyar Alh. Bola Ahmad Tinubu, a matsayin shugaban kasa a zaben game gari mai zuwa na 2023.” a cewarsa.

Gwamna Mai Mala ya kara da cewar “Bola Tinubu, da Bisi Akande jiga-jigai ne a jam’iyyarmu ta APC, don haka duk wani abu da za a yi na jam’iyyar sai an tuntubesu.”

Ya ce, “Duk wadanda ke cewar Shugaba Buhari shi ne matsalar jam’iyyar su bashi da masaniyar halin da jam’iyar ke ciki.”

Da aka tabo maganar da ta shafi ‘Zoning’ wato karba-karba kuwa, sai ya ce “ba a fara maganar ba sai zuwa gaba, don haka fitar da Shugaban kasa da shugaban jam’iyyar, sai nan gaba za a fara tattauna wadannan batutuwa”

A bangare daya kuwa ya kara da cewar “talakawan Najeriya ba za su manta da irin mawuyacin halin da jam’iyyar PDP ta jefa ‘yan kasar ba.”

“Lallai talakawan kasar nan ba za su manta da irin wahalar da suka shigaba lokacin mulkin PDP ba, don haka Shugaba Buhari na iya bakin kokarin wajen ganin ya fitar da talakawan kasar daga mawuyacin hali.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here