Sufeto Janar na Yan Sanda Ya Nemi Kotu tayi Watsi da Karar da Tsohon Sarkin Kano Ya Shigar Gaban ta

0
207

Daga Salisu Hamisu Ali

Babban Sufeto Janar na Yan Sanda na Kasa Mohammed Adamu ya bukaci babbar kotun tarayya dake Abuja da ta kori karar da tsohon sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi ya shigar yana kalubalantar tsare shi da aka yi.

A bayanan da Babban sufeton na yan sanda ya shigar yace kotun bata da hurumin sauraran karar.

A ranar 9 ga watan Maris dai da ya gabata ne dai gwamnatin Jihar Kano ta sauke Sanusi daga matsayin sarkin Kano sannan jami’an tsaro suka tafi da shi zuwa Abuja.

Daga bisani an kai shi garin Awe dake Jihar Nasarwa inda aka tsare shi a wani gida zuwa ranar 13 ga watan Maris bayan kotu ta bada damar sakin sa.

A karar da Sarki Sanusi ya shigar ta hannun Lauyan Sa Latif Fagbemi (SAN) ya bayyana cewa tsarewar da aka yi masa taci karo da hakkin sa na zirga-zirga da sauran hakkokin sa.

Sai dai Babban Sufeto Janar na Yan Sandan yace a jihar Kano Sanusi yakamata ya shigar da kara ba Abuja ba.

Mai Shari’a Chikere dai ta fitar da ranar 20 ga watan October domin sauraran karar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here