Masarautar Kano:Ganduje Na Son Majalisa ta Amince da Aminu Babba cikin Masu nada Sarki

0
211

Daga Salisu Hamisu Ali

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Gamduje ya nemi Majalisar dokokin jihar Kano da tayi gyara a dokar masarautu ta jihar ta shekarar 2019 domin sanya wasu hakimai guda biyu cikin masu nada sarki.

Shugaban Majalisar dokokin ta Kano Abdul’aziz Garba Gafasa ne ya sanar da hakan yayin zaman majalisar a ranar Larabar da ta gabata.

Ana sa ran yan majalisar za su bayyana matsayar su kan bukatar gwamnan kafin karshen wannan watan na Yuli.

Hakiman dai sun hada da Aminu Babba-Dan agundi ‘Sarkin Dawaki mai tuta’ da Sanusi Ado Bayero ‘Chiroman Kano’ dukkanin su dai a baya Sarkin Kano Ado Bayero da tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ne suka sauke su daga matsayin su bisa zargin kin biyayya.

Babba Dan Agundi ya Qalubanci sauke shi da Ado Bayero yayi a gaban Kotu. Sai dai bayan shafe tsawon shekara 17 kotun koli ta tabbatar da korar ta sa da marigayi sarkin Kano Ado Bayero yayi.

Bayan sake nada Aminu Babba a matsayin Sarkin Dawaki Babba da sabon sarkin Kano Aminu Ado Bayero yayi Gwamna Ganduje ya nemi majalisar dokoki ta Kano tayi garambawul ga dokar masarautu domin bawa Aminu Babba damar zama daya daga cikin masu nada sarki sai kuma Sanusi Bayero wanda tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya sauke.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here