Majalisar dokokin jihar Kano ta yi dokar kula da tsarin tafiyar da harkokin kuɗaɗe

0
203

Daga Abubakar zaharadden

Yayin da gwamnatin jihar Kano ta rage kasafin kudinta na bana da kimanin naira biliyan 70 saboda mummunan tasirin da annobar cutar korona ta yi ga tattalin arzikin jihar, majalisar dokokin jihar ta zartar da sabuwar dokar kula da tsarin tafiyar da harkokin kudaden gwamnatin jihar.

Sai dai kungiyoyin rajin shugabanci na gari na cewa, batun samar da doka lamari ne mai sauki, amma aiwatar da ita shi ne kalubalen.

Samar da sabuwar alkiblar tafiyar da kudaden gwamnati bisa tsarin dimokaradiyya na daga cikin manufar sabuwar dokar a jihar Kano wadda tun a shekarun baya aka samar da ita a matakin tarayya da ma wasu jihohin Najeriya.

Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Kano, Honarabul Kabiru Hassan Dashi, ya shaida wa manema labarai cewa, dokar za ta bai wa ma’aikatu da gwamnatin jihar ka’idar yadda za su kashe kudadensu, tare da yadda jihar za ta kasafta kudinta.

Yanzu haka dai kungiyoyin rajin shugabanci na gari sun yi maraba da wannan doka, muddin dai za a bita sau da kafa.

Daraktan kungiyar Organization for Community Civic Engagement mai shelkwata a jihar Kano, Comrade Abdulrazak Alkali ya ce suna fatan jami’an gwamnati, da gwamnatin jihar za su aiwatar da dokar yadda ya kamata.

To amma kwamishinan kudi da harkokin tattalin arziki na jihar Kano Alhaji Shehu Na’Allah ya ce sun shirya sosai domin aiki da dokar ka’in da na’in.

Tuni dai gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu akan wannan sabuwar doka a karshen makon da ya gabata kuma nan take ake sa ran za ta fara aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here