Kamfanin Arik Air Zai Fara Zirga-Zirgar Jirage a Kano

0
170

Daga Salisu Hamisu Ali

Kamfanin zirga-zirgar jirgin sama na Arik Air a yau Litinin ya sanar da cewa jiragen sa za su fara sauka da tashi a filayen sauka da tashin jirage na Malam Aminu Kano da na Yola a Jihar Adamawa daga Ranar 28 ga Watan Yuli.

Adebanji Ola, jami’in sadarwa na kamfani shine ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jihar Lagos inda yace dukkan ayyukan kamfanin zasu fara ne daga filin tashi da saukar jirage na Nnamdi Azikiwe dake Abuja tare da hadin gwiwar filin tashi da saukar jirage na Murtala Muhammed dake Lagos.

Mista Ola yace Kamfanin na Arik Air zai dinga aiki tsakanin Abuja zuwa Kano da Yola.

“Jirage daga Abuja zuwa Kano zasu dinga tashi sau Hudu a sati, a ranakun Litinin, Laraba, Juma’a da Lahadi yayin da Jirage daga Abuja zuwa yola zasu dinga aiki sau uku a sati wato Talata, Alhamis da Asabar.

” Kamfanin ya tabbatarwa da fasinjoji cewa za’a kare lafiyar su kamar yadda aka sanya ka’idojin kariya daga cutar COVID-19.

Mista Ola Ya Kuma bukaci Fasinjoji su dinga amfani da safar rufe hanci da baki sannan su kasance a filayen jirgin sama awa daya kafin lokacin tafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here