
Daga Abubakar zaharadden
Gwamnatin tarayya (FG) ta sanar da cewa za a bude makarantun sakandire a fadin kasar nan domin bawa daliban da ke matakin shekarar karshe damar zana jarrabawar kammala karatun sakandire (WASSCE).
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta fitar a yau, Litinin, ta bayyana cewa za a bude makarantun ne daga ranar Talata 4 ga watan Agusta 2020.