Babu Gudu Babu Ja da Baya wajen Karbo rance don aikin titin jirgin kasa a Kano

0
184

Daga Salisu Hamisu Ali

Gwamnatin jihar Kano tace babu gudu ba ja da baya a kudurin ta na ciyo bashi domin gina hanyar jirgin kasa a cikin kwaryar birnin Kano inda gwamnatin tace bayan alfanun da za a samu daga aikin zai kuma taimakawa harkokin kasuwanci da zirga-zirga cikin sauki.

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai Malam Muhammad Garba ya fitar kuma aka aikowa Jaridar PRIME TIME NEWS a yau Litinin a wani martani ga kungiyar Kwankwasiyya sanarwar tace babu wani nau’in suka da zai sa gwamnatin jihar ta dakatar da aikin wanda manufar sa shine mayar da Kano kasaitaccen Birni.

Tunda farko dai , Aminu Abdulssalam wanda yayi takarar mataimakin gwamna a zaben shekarar 2019 a jami’iyyar PDP wanda kuma a yanzu shine mai magana da yawun kungiyar Kwankwasiyya yayi wa manema labarai jawabi a Abuja yayi yunkurin sukar shirin aikin da gwamnatin ke son yi.

Kwamishinan Yada Labarai Malam Muhammad Garba yace tun da har bankin Kasar China ya amince da bayar da bashin , gwamnati kuwa za ta tabbatar an gudanar da aikin , sannan yan majalisar dokokin jihar sun amince da fara aikin kashi na farko da zai fara daga Kasuwar Dawanau zuwa Bata sannan kuma a kammala shi cikin watanni 20.

Malam Garba yayi bayanin cewa dukkan hanyoyin da suka dace anbi su wadanda suka hada da bada damar yin aikin daga majalisar dokokin jihar Kano da kuma sahalewa daga hukumomin gwamnatin tarayya da majalisar wakilai ta kasa.

Kwamishinan yace matsayin da Kwankwasiyya ta dauka akan aikin bai zo da mamaki ba la’akari da cewa kungiyar ba ta farin ciki da dukkan wani abu da gwamnatin APC ke yi komai kyan sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here