An Soke Bukukuwan Sallah a Jihar Niger

0
175

Daga Salisu Hamisu Ali

Gwamnatin Jihar Niger ta soke dukkanin bukukuwan Babbar Sallah.

Bukukuwan sun hada da hawan sallah na sarakunan gargajiya, sallar idi a filayen idi tare da gaisuwa da ziyarce-ziyarce.

A sanarwar da gwamnatin ta fitar a yau Lahadi ta bada umarnin gudanar da sallar idi a masallatan juma’a.

Sanarwar wacce take dauke da sa hannun Alhaji Ibrahim Ahmed tace za’a gudanar da Sallah a masallatan juma’ar ta hanyar bin ka’idojin kariya daga cutar COVID-19 wadanda suka hada da bada tazara, wanke hannu.

Sanarwar ta kara da cewa “Yayin da gwamnan ya bayar da damar yin sallar idi a masallatan juma’a a fadin jihar hakan zai kasance ne bisa bin tsarin ka’idojin kariya daga cutar COVID-19.

” matakin da aka dauka hana bukukuwan sallah na daga cikin kokarin da ake na hana yaduwar cutar.

Sanan gwamnatin jihar ta bukaci Al’umma da suyi amfani da lokacin bikin sallar wajen kara yin addu’o akan Allah Madaukakin Sarki ya kawo karshen Cutar da kuma matsalolin tsaro da ake fuskanta a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here