Na Tsani Cin Hanci da Rashawa – Kwankwaso

0
266

Daga Salisu Hamisu Ali

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso a yau Asabar yace yayi murabus ne daga hukumar bunkasa yankin Niger Delta(NDDC) a shekarar 2010 saboda halayyar cin hanci da rashawa a ma’aikatun gwamnati.

Inda yace hakanan na faruwa ne saboda gazawar shugabannin hukumomin.

Kwankwaso wanda tsohon dan takarar shugaban kasa ne yayi murabus a hukumar NDDC a shekarar 2010.

Kwankwaso yace yayi murabus ne daga hukumar ne saboda masu aikata cin hancin a hukumar inda yace “Ba zai so ya kasance yana daga ciki ba”.

Kwankwaso ya fadawa gidan Rediyon BBC Hausa cewa ” Cin hanci da rashawa na faruwa ne a NDDC saboda hadamar da wasu jami’an gwamnati keyi na tara kudade”.

“Duk Wadannan Abubuwan na faruwa ne saboda shugabanni basa kula sosai” cewar tsohon gwamnan.

Idan za’a iya tunawa dai majalisar wakilai ta kasa na bincikar badakalar kudi da ake zargin an tafka a hukumar ta NDDC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here