Kar Ku dauki Fasinjar da bai sa safar rufe Hanci da Baki Ba – Ganduje Ya gargadi masu ababen hawa

0
183

Daga Salisu Hamisu Ali

Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya gargadi matuka ababan hawa akan daukar fasinja wanda bai sa safar rufe hanci da baki ba.

Gwamnan yayi gargadin ne yayin kaddamar da rabon safar fuska da baki ga kungiyoyi wanda aka gudanar a gidan gwamnatin Kano yau Lahadi.

Gwamnan yace gwamnatin jihar tayi la’akari da cewa mutane basa son sanya safar rufe hanci da baki wacce kuma itace hanya mafi sauki domin kariya daga cutar COVID-19.

Sannan yace yaki da cutar na bukatar hadin kan kowa da kowa shi yasa gwamnatin jihar ta shigo da kungiyoyi da masu ruwa da tsaki wajen kawo karshen cutar.

“Mun shigar da Dukkan hukumomin tsaro, yan kasuwa, kungiyoyin matuka babura, masu masarautun gargajiya, malamai da kungiyoyin dalibai a cikin yaki da cutar.” Inji Ganduje.

Sannan ya kara da cewa ” Saboda haka ne muke raba safar rufe hanci da baki ga dukkan wadannan kungiyoyi, ina amfani da wannan damar wajen kira ga masu sana’ar tuka ababan hawa da su tabbata an bi ka’idojin yaki da cutar corona”.

“Dole kuyi amfani da ita yayin da kuke aiki , sannan dole ku tabbata fasinjojin ku sun yi amfani da ita, duk fasinjan da yaki sanya safar ta rufe hanci da baki kada ku dauke shi, domin gujewa karya doka.

” Muna da kotun tafi da gidan ka wacce ke hukunta wadanda suka karya wannan doka” inji shi.

Ganduje ya bayyana farin cikin sa kan yadda ake samun karancin masu kamuwa da cutar a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here