Cutar Korona: An Samu Karancin Yin Rijistar Haihuwa – NPC

0
179

Daga Salisu Hamisu Ali

Hukumar Kula da yawan jama’a ta kasa (NPC) ta koka kan karancin yin rijistar haihuwa a dai-dai lokacin da bayanai suka nuna cewa an samu karancin yin rijistar haihuwa cikin watanni hudu da suka gabata.

Daraktan hukumar na jihar Naija Dr. Usman Baba ne ya bayyanawa manema labarai hakan a garin Minna inda yace annobar COVID-19 ce ta haifar da rashin yin rijistar haihuwa a jihar.

Yace Annobar COVID-19 wacce ta sanya aka kafa dokar hana zirga-zirga ta ragewa hukumar kokarin ta na yin rijistar haihuwa a jihar.

“Rijistar haihuwa tayi karanci a yayin dokar kulle. Hakan ya faru saboda yawancin unguwanni na cikin dokar kullen , musamman yankunan kauyuka”.

” Cutar COVID-19 ta hana mata zuwa wajen duba lafiya wanda hakan yasa da yawan su sun haihu ne a gida” a cewar sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here