An Tallafawa Tubabbun Mayakan Boko Haram da Kayayyakin Sana’o’i

0
230

 

Daga Salisu Hamisu Ali

Hukumar bunkasa cigaban yankin Arewa maso yammaci kasar nan, NEDC ta tallafawa mayakan Boko Haram wadanda suka tuba suka ajiye makaman su, kuma suka samu horo na watannin 6 .

Abba Musa, shugaban hulda da jama’a na hukumar ne ya gabatar da kayan tallafin amadadin shugaban hukumar, Mohammed Alkali yayin bikin yaye yan rukuni na 4 na tubabbun mayakan a Sansanin Malam Sidi .

Mr. Musa yace kayayyakin da aka tallafa musu sun hada da injin yin walda, kayan aikin kafinta, kayan aski da injin wanki.

Sannan yace dalilin da yasa aka raba kayan tallafin ga tsofafin mayakn shine domin su zama sun dogara da kan su a yayin da zasu koma cikin al’umma bayan sun samu horo kan sana’oi.

Sannan ya bukaci wadanda suka amfana da tallafin da suyi amfani da shi ta hanyar da ya dace domin bunkasa rayuwar su ta nan gaba.

Yayin da yake jawabi a wajen bikin Gwamnan jihar Gombe Inuwa Yahaya ya jinjinawa tubabbun mayakan bisa karbar zaman lafiya tare da zama masu amfanar al’umma.

Mr. Yahaya wanda ya samu wakilcin mataimakin sa Mr Manneseh Jatau , ya nemi wadanda suka amfana da shirin da su taimaka wajen bunkasa cigaban kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here