Osinbajo Ya Qalubalanci Matasa yayin da ake Fama da Annobar COVID-19

0
189

Daga Salisu Hamisu Ali

Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo a yau Asabar ya buqaci matasan kasar nan da su yi amfani da damarmakin da suke samu kuma su zamo masu kawo mafita yayi da annobar Corona ta haifar da kalubale masu yawa.

Mataimakin shugaban kasar na fadin haka ne yayin taron yiwa daliban Edgewood Collage wadanda suka kammala makarantar jawabi wanda aka gudanar ta kafar sadarwa.

Osinbajo yace ” yanayi ne ke sa ka cigaba , ba wani mutum da yake anan kafin yanzu , babu wani daga cikin iyayen ku ko ni da zai fada muku yadda rayuwa zata kasance bayan wannan annobar da ta addabi duniya”.

Mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa matasa na da matukar muhimmanci a irin wannan lokaci wanda ake samun damarmaki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here