Kungiyar Likitoci Za ta Koma Yajin Aiki

0
140

Daga Salisu Hamisu Ali

Kungiyar Likitoci ta Kasa a yau Asabar ta bawa gwamnatin tarayya wa’adin makwanni uku domin ta duba bukatun ta ko kuma ya’yan kungiyar su tsunduma yajin aiki a ranar 17 ga watan Agusta.

Shugaban kungiyar na kasa, Dr. Aliyu Sokomba ne ya sanar da hakan yau a Abuja a wani taron manema labarai.

Shugaban kungiyar likitocin ya karanta bayanan taron da majalisar koli ta kungiyar ta gudanar a hotal din Gombe International tsakanin 20 ga watan Yuli zuwa 25 ga watan.

Dr. Aliyu yace “Majalisar Koli ta kungiyar ta yanke matsaya akan cigaba da dakatar da yajin aikin da muka fara zuwa sati uku domin bawa gwamnati dama ta duba bukatun mu, rashin duba bukatun namu ka iya sa mu koma yajin aiki a ranar litinin 17 ga watan Agusta.

Sannan yace kungiyar ta nemi a biya su alawus na musamman da ake bayarwa kan annobar COVID-19 , Sannnan sun yi kira da majalisar wakilai ta kasa tayi bincike kan yadda ba’a sanya ma’aikatan lafiya ba cikin tsarin inshora.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here