Kano: Shugaba Buhari zai buɗe gadar Dangi

0
261

Daga Abubakar zaharadden

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai bude gadar sama mai hawa biyu hade da titin ƙarkashin ƙasa na shataletalen Dangi a Kano wanda gwamnatin jihar ta kashe naira biliyan 4 wajen gudanar da aikin.

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan da yammacin jiya Juma’a yayin da ya kai ziyara wajen da aka gudanar da aikin domin duba yadda yake gudana.

Gwamnan ya ƙara da cewa, aikin ba zai dakata ba duk da cewa an shiga halin annobar COVID-19 a faɗin duniya wadda har ta kai ga cewa ta bullo jihar Kano kuma ana samun nasara wajen yaƙin da ake yi da annobar tare da cewa an yi aikin ne domin mutanen Kano su mora.

Haka kuma gwamna Ganduje ya ce abun jin dadi shi ne yadda aka kammala aikin wanda aka kashe biliyan 4 kuma akan lokacin da aka ɗibar masa.

Ya ƙara da cewa, ”Yin wannan aiki wani ɓangare ne na abubuwn da gwamnatina ta ƙudurn yi domin jihar Kano ta goga da sauran takwarorinta manyan biranen duniya ta fuskar ababen more rayuwa”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here